/

Bayan rufe masallatan Abduljabbar, masu yaɗa wa’azin sa ma sun shiga tarkon gwamnati

Karatun minti 1
Sheikh Abdujjabar

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rufe dukkannin masallatai da wuraren karatu ko taro na Shaikh Abduljabbar Shaikh Nasiru Kabara bisa zargin zagin yin kalamai masu barazana ga tsaron jihar.

Sanarwar da ta iske Dabo FM cikin wata takarda da kwamishina yaɗa labaran jihar, Malam Muhammadu Garba ya rattabawa hannu, ta ce;

“Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe masallacin Sheikh Abduljabbar da dukkannin inda ya ke wa’azi saboda dalilan tsaro.”

Haka kuma ya ƙara da cewa; “Ko ka dora karatunsa a kafafen sada zumunta, ko kuma mu samu wani ma yana tura karatunsa, hukunci ya hau kan mutum.

Tin a ƴan makonnin da suka gabata, malamai suka yi ta yin Allah wadai tare da jan hankalin mahukunta domin a dakatar da malamin daga yaɗa irin kalmomin da a cewarsu take baƙanta wa musulmai.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog