Sharuɗan da masu buƙatar aikin koyar da Hausa a Amurka za su cika

dakikun karantawa

Bayan rahoton DABO FM kan yadda gwamnatin Amurka take neman malaman da za su koyar da Hausa da Yarabanci, mun zaƙulo sharuɗan da masu nema za su cika.

Gwamnatin ƙasar ta ce tilas ne masu neman aikin su kasance ƴan Najeriya, masu fasfo kuma su kasance suna Najeriya a lokacin da za su nemi aikin.

DABO FM ta tattara cewa daga ranar 1 ga Fabarairu za a fara neman aikin za kuma a rufe ranar 1 ga watan Yuni, 2021.

Ga wasu daga cikin sharuɗan;

  •  Dole ne masu neman aikin su kasance masu digiri a fannin Turanci, Ilimin koyarwa, Yarurruka, Yarabanci, da Hausa.
  •  Dole masu neman aikin su kasance malaman Turanci, Yarabanci ko Hausa a jami’o’i, makarantun gaba da sakandire kuma su kasance suna da ƙwarewa a fannin koyarwa.
  •  Dole su sadssmu shaidar da ta nuna an gamsu da su a wajen da suke aiki.
  • Dole ne mai buƙatar aikin ya ci kashi 90 na daga jarabawar ƙwarewa  a Turanci ta yanar gizo ‘ Internet TOEFL Test.’
  • Dole ne mutum ya zama na gari kuma babban jakadan ƙabilar da yake wakilta kuma a tabbatar za a zauna da mutane lafiya.
  • Dole ne mutum ya mayar da hankali wajen kammala aikin da za a dora masa har ya dawo gida.
  • Dole mai buƙata ya kasance yana da ilimi mai zurfi a yaren Hausa  tare da sanin abubuwan da suke wakana a Najeriya, kana ya kuma zama mai sha’awara koyar da Hausa da al’adunta a ƙasar Amurka.
  • Dole ne mutum ya zama ya kware a bada kwarin gwiwa.

A danna a kan shuɗin rubutun nan domin neman aikin tare da karin bayani.

ɗ ƙ

Amurkan ta ce za ta yi wa dukkanin waɗanda suka samu aikin kuɗin jirgin zuwa da dawowa na ƙasar, za ta riƙa basu kudaden kashewa na wata-wata, ci da shansu da kuma inshorarsu ta lafiya.

Sai dai ta ce ba za ta ƙauki nauyin iyalan mutum ba, hasalima ba za a bari kowa ya tafi da iyalansa ba, ko da kuwa mutum zai ɗauki nauyin iyalansa da kansa.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog