Ku nemi rijistar zaɓe don kawo gwamnatin da za ta yi mana adalci – Sheikh Abduljabbar

Karatun minti 1

Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi kira ga magoya bayansa da su nemi katunan zaɓe domin sauya gwamnatin APC a zaɓe mai zuwa.

DABO FM ta tattara cewa a jiya ne dai gwamnatin jihar ta haramta wa malamin yin wa’azi tare da rufe masallatansa a faɗin jihar Kano.

A cikin wata hira da malamin ya yi da sashin Hausa na BBC jim kadan bayan umarnin gwamnatin, ya ce ya miƙa wuya ga umarnin gwamnatin jihar.

Kazalika ya yi kira ga ɗalibansa da su nemi katunan zabe domin kawo gwamnatin da a cewarsa za ta yi musu adalci.

“Magana ce ta shekara biyu, ku je ku yi rijistar zaɓe in dai da gaske ku ke yi, yawanku ya isa ku sauya gwamnati. Wannan kawai shikenan.”

Da yake amsa tambayar ko zai fito takara, ya amsa da cewa “A’a ba zan fito ba amma na san za a samu masu adalcin da za si fito waɗanɗa za su mana adalci.”

“Mu basu kuri’a su yi mana adalci, su ma kuma wadanda su ke mana zaluncin su ɗanɗana kuɗarsu.”

Ya ce gwamnatin jihar ba ta masa adalci ba domin ba a kirashi domin kare abubuwan da yake faɗa ba.

Ana dai zarginsa da yin kalamai masu tayar da hankalin al’ummar jihar Kano.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog