(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Budaddiyar wasika zuwa Hon. Aminu Suleiman Goro, Daga Umar Aliyu Fagge

dakikun karantawa

Bayan sallama irin ta addinin musulunci tare da fatan kasancewar ka cikin koshin lafiya, ina mai amfani da wannan damar gurin isar da sakon al’ummar Karamar Hukumar Fagge kamar haka:-

Rahotanni daga kafafen watsa labarai musamman facebook sun rawaito cewa ka shirya gangamin taron bada jari ga mata da maza guda dari biyar, taron da aka ringa kwarzantawa cewa babu kamar shi amma abin takaici da ban haushi sai wannan taron bada tallafin yafi kamanceceniya da taron tozarta alumma da ita kanta karamar hukumar fagge a idon duniya.

 

A fahimtar mu wakili nagari mai kishin alumma shi ne mai sauraren bukatar wannan alumma don aiwatar da abin da suke bukata na cigaba, ba wai abin da yaga damar aiwatarwa ba a matsayin shi na wakilin alumma. Idan har da gaske ne cewa wannan wakilin yana son cigaban alummar karamar hukumar fagge me ya hana ya aiwatar da taron bada tallafi/tozarci ga mutanen da ya dace da kuma abin da yafi kyautuwa?

 

Inda wannan wakili yana son cigaban alumma kamata yayi a bangaren mata a dauki jarin kayan abinci a basu kamar:- Shinkafa,  Wake, Taliya, Macaroni da Man gyada domin dogaro da kai kuma su rike iyalan su. Wasu daga cikin matan kuma a samar musu da Waken suya da Mai domin kama sana’a ka in da na in.

 

Bangaren maza kuwa wannan wakilin yana kokarin nunawa duniya cewa samarin wannan unguwa basu fahimci inda duniya ta dosa ba domin ko dan majalisar kauye bazai kawowa alummar sa injin markade na dauri a matsayin abin cigaban rayuwa ba, keken dinkin ma ba na zamani ba ne a daidai lokacin da ake canja  komai daga manual zuwa digital amma mu kuma giyar baya ake kokarin saka mana.

 

Sanin kowa ne cewa sana’ar dinki samarin wannan unguwa suka yi fice a kai,  to me zai hana wannan wakilin ya kai kudurin da gwamnati zata samar da wani kamfanin dinki a wannan karamar hukuma domin amfanin kowa da kowa?

Tabbas samar da wannan kamfanin dinki zai taimaka gurin samar da aiki ga daukacin yan karamar hukumar tare da samun kudin shiga daga sassan gwamnati ga alummar wannan unguwa.

 

Uwa uba ana zargin wannan wakili da nuna halin ko in kula gurin tallafawa dalibai yan wannan karamar hukuma gurin neman ilimi ta kowace fuska, duk da cewa shi yake rike da kwamitin ilimi mai zurfi a wannan kasa tamu ta gado.

 

A karshe ina amfani da wannan damar gurin jan hankalin mutanen wannan karamar hukuma da mu tashi tsaye gurin sanin hakkokin mu suka rataya a wuyan kowane wakili tare da nuna musu cewa komai wani wakili yayi musu ba alfarma bace dama nauyin da ya rataya ne a wuyan shi don haka babu bukatar ace sai ya tara mutane ballantana har ya tozarta su akan abin da bai taka kara ya karya ba.

 

Umar Aliyu Musa
[email protected]
07039317790

Karin Labarai

Sabbi daga Blog