(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

#EndInsecurityNow: Yadda aka yi wa Ali Nuhu rubdugu a Twitter

Karatun minti 1

Jarumin Kannywood Ali Nuhu ya na shan rubdugu daga matasan arewacin Najeriya a shafin sada zumuntar nan na Twitter.

Hakan na zuwa ne sakamakon furucin da jarumin ya yi kan rashin shigarshi zanga-zangar #EndInsecurityNow da aka shirya a Arewa domin ceto yankin daga matsalar rashin tsaro.

DABO FM ta tattara cewa; A wata hira da Ali Nuhu ya yi da sashin Hausa na rediyon DW, Ali Nuhu ya ce sukar da ya ke sha daga wajen ‘yan Twitter ce ta sanyashi bai shiga zanga-zangar ba.

“Wani lokacin sai kaga kamar ma kai a matsayinka na Tauraro in za ka shiga maganar kamar shisshigi za ka yi wa mutane, kaje Twitter, a nan ne za ka ga an sa taurarin Arewa, a zage su a kushe shu ayi musu wulakanci yadda rai yake so. Haka zalika a Facebook da Instgram.

Wannan shi ne dalilin mutane suke ja ba ya ba wai don ba sa son shigowa bane.”

Sai dai furucin jarumin ya kara hasala masu amfani da shafin Twitter wajen yi masa raddi da wasu suke ganin an yi masa ‘kaca-kaca.’

Ga wasu daga cikin irin martanin da aka yi wa jarumin.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog