Ali Nuhu yana rabon miliyoyi a Instagram

Karatun minti 1

Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu ya na rabon miliyoyin kudi a shafinsa na Instagram.

Ali Nuhu yana raba Naira dubu dari-dari da kuma Naira dubu dari da hamsin-hamsin ga masoyansa wadanda suka taka rawa a gasar wakar ‘Dogara Ya Dawo’ da suka sanya a watannin baya.

Wakar Dogara Ya Dawo waka ce da mawaki Dauda Rarara ya rera wa tsohon Kakakin majalissar Tarayya, Hon Yakubu Dogara.

DABO FM ta tattara cewa a halin yanzu karfe 2:55 na rana, jarumin ya raba Naira miliyan 2 da dubu hamsin ga masoyansa sama da mutum 20.

Rarara ne ya sanya gasar, Ali Nuhu yake raba kudaden.

Ga wasu daga cikin hotunan racitan tura kudin da jarumin yake sanya wa a shafinsa na Instagram.

Shaidar wadanda aka ba wa Naira dubu dari da hamsin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog