Copyrighted.com Registered & Protected

Buhari ya fara bada mukamai ga wadanda ya sawa takun-kumi akan cin hanci da rashawa

Shashin Hausa na jaridar Premium Times ta rawaito cewa;

” Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nada tsohon Ministan Cinikayya, Bello Maitama-Yusuf a matsayin daya daga cikin mambobin Hukumar Daraktocin Jiragen Kasa na Najeriya (NRC).

Bello mai shekaru 72, an taba zargin sa da cin rashawa a zamanin mulkin soja na Shugaba Muhammadu Buhari, a cikin 1984.

Wannan ya sa Bello ya fice daga Najeriya, ya nemi mafaka a kasar waje.

Cikin 1979 Bello ya rike mukamin Ministan Harkokin Cikin Gida, sannan cikin 1982 aka maida shi Ministan Cinikayya.

Bello da marigayi Umaru Dikko sun kasance a sahun farko na jerin sunayen wadanda suka gudu daga Najeriya, kuma gwamnatin mulkin soja a lokacin ta neme su ruwa a jallo.

Bayan sama da shekaru 30, a yanzu an nada shi mamba na Hukumar Daraktocin Kula da Jiragen Kasa.

Takardai shedai aiki

Ibrahim Hassan ne shugaban hukumar, sauran mambobi sun hada da Kayode Opeifa, AIG Umar Ambursa, Obiarari Nnamdi da sauran su.

Masu Alaƙa  Kisan Kolade Johnson abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske - Shugaba Buhari

Gwamna Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ne ya bada sunan sa, shi kuma Buhari ya amince.

Haka Kakakin Yada Labarai na Badaru a fannin Soshiyal Midiya, Auwal Sankara ya rubuta a shafin san a Facebook.

Ya ce an nada Bello Maitama saboda “kwazon sa da juriya da kuma aiki tukuru wajen tsayawa tsayin-daka domin ci gaban jam’iyyar APC da kuma ciyar da Najeriya da Jihar Jigawa gaba.”

Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya kaddamar da hukumar daraktocin tun a ranar Alhamis da ta wuce.

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: