Labarai Taskar Malamai

‘Corona Virus’ shirin Yahudawa ne domin su hana Musulmai ibada – Sheikh Jingir

Shugaban kungiyar IZALA JOS, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bayyana annobar ‘Corona Virus’ da ta addabi duniya a matsayin shirin Yahudawa wanda a cewarshi an kirkireta domin hana addinin Musulunci a fadin duniya.

Sai dai DABO FM ta tattara cewar annobar ‘Corona Virus’ tafi illa a kasashen China da Italiya. Bincike ya nuna Musulman dake China basu da kashi 1 na yawan al’ummar dake rayuwa a kasar, a kasar Italiya kuwa musulmai na da kashi 2.3 kacal.

A wani taro da malamin yayi da manema labarai yace baya goyon bayan rufe wuraren ibada da akayi a fadin duniya tare da shirin da akeyi na fara rufewa a Najeriya.

“Na kirawo ne domin in fada muku fahimtarmu ta Musulunci akan wannan abin,”

“Da ‘Corona Virus’ da Kuturta da Malaria, ba abinda zai iya samunmu sai Allah ya rubuta zai same mu, wannan rigima ce ta neman tattalin arziki da ake yi tsakanin China da America. Mu musulmi kada mubi tururuwar Iblis.

“Dama Ubangiji ya fada mana halinsu cewar bazasu gushe ba sai suna yakarku domin kubar addiniku, sai sun maida ku baya kunyi ridda.”

“Ni a guri na, ‘Corona Virus’ karya ce.”

“Meya hada gwamnatoci da hana taba don domin su hana musulmi, su raba Musulmi da Sallah su rabasu da Dawafi da aikin Hajji.”

Duk da tabbaci samun cutar a kasar Saudiyya da wasu kasashen musulmi, malamin yace ba’a samu cutar a kasashen ba.

“Annobar nan babu ita a Makkah, babu ita a Najeriya da Niger, to babu dama ayi mana hukunci annoba. Basason ayi dawafi da aikin Hajji shiyasa aka rufe haramin Makka da Madina.”

Malamin yayi jawaban ne bayan soke sallar Juma’a da gwamnatin jihar Kaduna tayi domin tsoron yaduwar cutar a cikin al’umma.

Daga karshe malamin yayi kira ga kasashen Musulmai musamman kasar Saudiyya da ta bude masallatan Harami da na Madina domin cigaba da gudanar da ibada kamar yadda a cewarshi; “addini ya tanada.”

DABO FM ta tattara cewar gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe filayen jirage na jihohin Kano, Fatakwal da Enugu.

Haka zalika ma’aikatar Ilimi ta kasa ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun tarayyar Najeriya na tsawon kwanaki 30.

Masu Alaka

Yazamana dole ‘yan siyasa sun girmama Sarakunan Gargajiya – Dr Pantami

Dabo Online

Hotuna: Ziyarar CP Wakili ga wasu daga cikin manyan Malaman jihar Kano

Dabo Online

Komawa ga Allah ne mafita a halin da Najeriya ke ciki – Sheikh Rabi’u Zariya

Mu’azu A. Albarkawa

Zagin Shuwagabanni da Malaman Addini tamkar zubar da jini ne – Dr Rijiyar Lemo

Dabo Online

‘In da Jonathan ko wani dan Kudu ne ke mulki, da an ce shirya kashe-kashe ake don cutar Arewa’

Dabo Online

In Sarki ya kira dan siyasa mutumin kirki, masu hamayya zasu ce yana goya masa baya – Dr Pantami

Dabo Online
UA-131299779-2