Labarai

Yanzu Yanzu: NNPC na garin Hadeja na siyar da litar Mai N143 da kwabo 80

Gidan man NNPC na siyar da man fetir naira 143 da kwabo 80, duk da dokar da gwamnatin tarayya tayi na rage man daga N143 zuwa N125.

‘Gidan NNPC da ya kasance mallakar gwamnatin Najeriya.’

Wakilin DABO FM da yayi tattaki har zuwa garin Hadeja dake jihar Jigawa ya tabbatar da cewa gidan man NNPC na garin Hadeja sun bijirewa umarnin gwamnatin sunyi gaban kansu.

Da yake tattaunawa da daya daga mahaukatan gidan man, wanda ya nemi mu sakaya sunansa saboda zai iya rasa aikin sa, ya bayyana wa DABO FM cewa Manajan gidan NNPC na Hadeja shine ya basu umarnin a siyar da litar a N143.80

Kofar garin yamma, Hadejia jihar Jigawa.
UA-131299779-2