Da Ɗumi-Ɗumi: Akwai yiwuwar El-Rufa’i ya naɗa mace Sarkin Zazzau

dakikun karantawa

Akwai yiwuwar gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya naɗa mace Sarkin Zazzau biyo bayan rokon da mai ɗakin gwamnan ta yi.

Rahoton Dabo FM ya bayyana wannan na zuwa ne bayan mai ɗakin gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza El-Rufa’i ta yi kira ga gwamnan da ya naɗa mace a matsayin Sarkin Zazzau.

Matar gwamnan ta yi kiran ne a shafin ta na Twitter ranar Juma’a 25 ga Satumba, ta ce : “A sha’awar dai-daito tsakanin jinsi (Maza da Mata), El-Rufa’i mai zai hana mu samu wata kamar Sarauniya Amina ta Zazzau.”

Amina Sarauniyar Zazzau, wadda ta rayu daga shekarar 1533 zuwa 1610, ɗaya ce daga cikin ‘ya’ya biyu da Sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa. Wato ita Amina ɗin da kuma ƙanwarta mai suna Zariya. Ta yi sarautar Zazzau bayan rasuwar mahaifinta, daga shekara ta 1509 zuwa 1522, wato shekarunta 13 ke nan a kan karagar mulki.

Ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, kuma ta shida a cikin sarakunan haɓe waɗanda suka yi mulki bayan Addinin Musulunci ya fara bayyana a ƙasar Zazzau. Har ila yau a cikin jerin sarakunan Zazzau gaba ɗaya ita ce ta 23.

Sarauniya Amina ta shahara matuƙa a ƙasar Hausa da ma yankunan da daular Usmaniyya ta mulka. Ta yi kai  wa da komowa na yaƙe-yaƙe a wurare da dama.

Sai dai mai dakin gwamna ta janye batun inda daga bisani ta ce; “Wai ku baku san wasa ba?.”

Har zuwa yanzu dai gwamna El-Rufa’i bai sanar da sarkin da zai gaji kujererar marigayi Sarki Shehu Idris ba, inda ya bayyana yana kan nazarin wasu littafai na tarihin yanda ake naɗin sarautar.

El-Rufa’i ya kuma bayyana an aike masa da sunan mutane goma sha daya (11), wanda a ciki ne zai tabbatar da ɗaya daga ciki a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog