(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

‘Adadin wadanda aka kashe a harin tawagar Zulum sun kai 30’

Karatun minti 1
Babagana Zulum - Gwamnan Borno (APC)

Wasu rahotanni da ake samu yanzu sun bayyana cewa adadin wadanda suka mutu sakamakon afkawa tawagar gwamna Zulum da ‘yan ta’adda suka yi sun kai 30.

Wasu majiyoyi ne suka shaidawa kamfanin Labarai na AFP.

DABO FM ta rawaito yadda mayakan Boko Haram suka afka wa tawagar Gwamna Zulum na Borno ranar Juma’a a kusa da garin Baga.

Majiyoyin sun shaidawa AFP cewar adadin sun karu ne a lokacin da ake cigaba da binciko gawarwakin wadanda suka mutu.

Sabon rahoton ya ce an kashe ‘yan sanda 12, sojoji 5, jami’ai masu goyon bayan gwamnati guda 4 da farar hula 9.

Adadin ya karu da kusan ninki biyu kan yadda aka rawaita a daren jiya Juma’a.

Har yanzu ana cigaba da binciken gawarwakin wadanda suka rasu rayukansu sakamakon harin, kamar yadda majiyoyin suka tabbatar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog