/

Jarumi Adam A. Zango ba shi da lafiya

Karatun minti 1
Jarumi Adam A Zango

Fitaccen jarumi kuma mawaki a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Adamu Abdullahi Zango da aka fi sani da Zango ba shi da lafiya, DABO FM ta tattara.

Jarumin ya wallafa sako a shafinsa na Instagram inda ya kira masoyansu da su saka shi cikin addu’o’i.

Sakon da ya wallafa Laraba, ya sanya da yawa daga cikin abokan sana’arshi yi masa addu’ar ‘Allah Ya baka lafiya.’

Mansur Isma’il da aka fi sani ya Mansoor Makeup ya ce; Allah Ya baka Lafiya Bossman. Shi ma wani daga cikin manyan yaran jarumin, Saifullah Isiyaku Idris ‘Safzor’ ya ce; Allah Ya kara lafiya Sir’.

Jarumi Adam Zango

Bayan tuntubar makusanta jarumin, sun tabbatar da DABO FM cewa jarumin ba ya jin dadi, sai dai basu bayyana mana abinda yake damunsa ba.

Tin daga ranar da ya wallafa yana neman addu’ar, har kawo yanzu bai sake wallafa komai ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog