(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Gwamnatin Ganduje zata biya ₦30,600 a matsayin mafi karancin albashi

Karatun minti 1
Dr Abdullahi Ganduje
Dr Abdullahi Ganduje

Gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tace zata biya ₦30,600 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikacin jihar Kano.

Sanarwar ta fito daga hannun babban mai baiwa gwamna Ganduje shawara fannin labarai, Fa’izu Albindiki.

“A shirye muke da mu biya albashin Naira 30,000 a duk wata saboda walwala da farin cikin ma’aikatanmu na sama da komai. Bayan nan kuma za mu ba shi muhimmanci a ko da yaushe.”

Tin farkon makon da muke ciki shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu domin maida Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashin duk wani ma’aikacin fadin tarayyar Najeriya.

Dokar dai ta bawa dukkanin ma’aikata damar shigar da kara ofishin Ministan Kwadago a duk lokacin da ma’aikatarshi ta gaza biyanshi N30,000.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog