(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Wani Mai gadi ya zabi ayi rijiyar burtsatse a kauyensu da a gina masa gida

Karatun minti 1

Wani Mai gadi ya mayar da kyautar gida da mai gidanshi dan kasar Indiya ya bashi domin kai bukatar yin rijiyar burtsate a kayensu.

Musa Usman, wanda yake da zama a garin Giljimma dake karamar hukumar Birniwar jihar Jigawa, yana zaune ne a gidan kasa mai shifci a sama.

Mallam ya kasance mai gadi a kamfanin maganin Mr Verghese a jihar Legas na tsawon shekaru 25, a daidai lokacin da Mallam Usman ya bukaci ajiye aiki domin komawa wajen iyalanshi, shugaban kamfanin yace za a gina masa gida domin nuna godiyar aikin da Mallam Usman yayi.

Sai dai Mallam Usman ya roki da a tonawa kauyensu rijiyar burtsatse maimakon a gina masa gida a kauyen bisa wahalar da yan garin sukeyi na neman ruwan sha.

Ya bayyana cewa yan garin nasu sukanyi tafiya mai nisa kafin nemawa kansu ruwan da zasu sha kafin akai ga na amfanin yau da kullum.

Tini dai al’ummar yankin suka fara farinciki da hukunci da Mallam Usman ya yanke na saukaka musu wahalar ruwa a yankin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog