Wasu Matan Arewa suna nemawa Mahaifiyarsu mai shekaru 60 miji a shafukan sada zumunta

dakikun karantawa

A cigaba da zakulo irin abubuwan da suke faruwa tsakanin Mata da mazan Arewa a shafukan sada zumunta, yau ma mun sake komawa manhajar Instagram inda mukayi duba a shafin Northern Blog.

Inda muka lalubo wata baiwar Allah data aiko zuwa shafin tana yiwa mahaifiyarta cigiyar mijin Aure.

Kamar yadda zaku gani a hoton kasa, matar ta bukaci a sakaya sunanta tace, tana so a taimaka mata domin nemowa mahaifiyarta yar shekara 60 mijin Aure, inda ta bukaci a nema mata dattijon kirki.

Tace dalilinta na turo da cigiyar mijin ga mahaifiyarta shine bisa rabuwar da mahaifinta sukayi da mahaifiyarta.

“Salam, Dan Allah Mamar mu suka rabu da Babanmu, to dan Allah in akwai wani dattijo mai neman mata. Dan Allah ki bicika mun ko za’a samu.”

“Amma fa tare da yaranta take, kuma gaskiya wanda zai somu tsakani da Allah, kuma wanda zai iya taimaka mata.”

“Wanda ka iya taimaka in ansamu, kiyi magana dashi muji. Nagode.”

“Allah ya biyaki ‘yar uwata, gaskiya ta kai 60, don ko ni da nike magana dake ‘yar ta ta fari na kai 40.”

A kokarin da mukayi na gano asalin baiwar Allah da ta aiko da wannan cigiyar, gano yar wana gari ce?

Sai dai bisa Hausar datayi amfani wajen aike sakon ya kusa bada tabbacin cewa ‘yar jihar Katsina ce.

Karin Labarai

Latest from Blog