Gwamnatin jihar Kano ta amince da muƙabala tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagororincin gwamna Ganduje ta amince da bukatar zama tsakanin malaman jihar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Babban sakataren yada labaran gwamnan jihar, Mallam Abba Anwar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.

Sanarwar ta ce gwamnatin ta amince da bukatar malamin domin yin adalci kamar yadda ya bukata.

Ya ce nan da wani lokaci kadan gwamnatin za ra sanar da ranar da kuma wajen da za a gudanar da tattaunawar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog