(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ko yaron da baya magana yasan waye Adamu Zango – Zango

dakikun karantawa
Jarumi Adam Zango

Shahararren jarumi da mawaki a masana’antar Kannywood, Adamu Zango ya kara bayyanawa duniya cewa shine jarumin da yafi kowanne suna a duniya.

Wannan ne karo na biyu da jarumin ya sake yin irin wadannan nan kalamai.

A yayin hirarshi da sashin Hausa na BBC, Zango ya kara tabbatar da maganarshi akan shine wanda yafi kowanne bahaushe suna a duniya, sai dai a wannan karon yace shi dama a harkar fim da wakoki yake nufi.

“Sheikh Dahiru Bauchi, Kabiru Gombe, Sarkin Kano, da Dangote, ai duk mai hankali bai kamata ya dauko su yace wai zai hadi ni dasu ba.”

“Me ya hada Dangote da harkar nishadantarwa?, Meya hada Ahmad Musa da nishadantarwa?, Dan kwallo ne mai suna a duniya.”

“Saboda haka ni nayi magana ne akan sana’ar da nake ciki, waka da fim.”

“Saboda haka idan karya nayi, sai ka fara daga cikin gidanku, kamar yadda na fada maka, ina da masoya, har da yaro wanda bai iya magana ba, idan ya kalle ni zai nuna ni. Idan wanda ya fara magana ne zai kira suna na.”

“A kan baro gari, uwa gari, anyi yafi sau dari da yara kawai , don akawo su wajen Adamu Zango.”

“Shekaru 2 da suka wuce, wani ya kirawo ni daga Rediyon DW, yace min sunyi bincike, sun gano cewa babu wani Bahause a cikin masana’antar Kannywood da yafini suna a duniya.”

“Nace ni bazan dorar da wannan maganar ba, saboda banaso ayi min cha, to amma wadanda suka kirani, in da sun wallafa wa duniya, meyasa zan tsaya ina fadaa duniya?”

“Abin da nasan cewa na kai, mai zai sa in kasa fitowa in fadawa duniya.?”, hakan da na fada yasa anyi binciken.”

“Duk wadanda suke cewa sun fini, to su fito da wata hujjar da ta nuna cewa sun fini.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog