Gwamnoni sun roki Buhari ya cire dokar bai wa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye

Gwamnonin Najeriya sun nuna rashin jin dadinsu ga sabuwar dokar bawa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye.

Sabuwar dokar dai zata baiwa kananan hukumomi damar cin gashin kansu, inda zasu rika karbar kudi kai tsaya daga asuusun gwamnatin tarayya.

Gwamnonin sunce dokar da sabawa kudin tsarin mulkin Najeriya a shekarar 1999.

Tuni dai gwamnonin suka aike da korafinsu zuwa ga fadar gwamnatin tarayya.

Sai dai a nasu bangaren, gwamnatin tarayya tace dokar tana nan babu gudu babu ja da baya.

Har ma anjiyo fadar gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dokar zata fara aiki ne 1 ga watan Yulin 2019.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Masu Alaƙa  Dokar baiwa kananan hukumomi 'yancinsu zata fara aiki 1 ga watan Yulin 2019

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: