/

Rarara ya ba wa Tijjani Asase ‘Sangami’ kyautar motar miliyoyin Nairori

Karatun minti 1

JAIPUR INDIA: Babban mawakin jami’iyyar APC a Najeriya, Dauda Adamu Rarara ya bai wa jarumi Tijjani Asase kyautar mota.

DABO FM ta tattara cewar mawakin ya mallaka wa Asase mota kirar Toyota Matrix yar zamani.

Motar da darajarta tana kai wa Naira miliyan uku da dubu dari tara, kamar yadda farashin yake a JiJi.ng, wata kasuwar Najeriya da ake siye da siyar da tsofaffin kayayyaki a yanar gizo.

Jaruma a masana’antar Kannywood, irin su Ali Nuhu da Aminu S Bono sun taya jarumi Tijjani Asase murnar samun kyautar daga Dauda Rarara.

Aminu S Bono ya wallafa a shafinshi na Instagram yana mai cewa; Muna yi maka murna, Allah Ya taya riko, shi kuma jami’ar waka, Dauda Kahutu Rarara, Allah Ya kara yalwata arzikinsa Ya kuma raya zuri’arsa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog