Babban gida, manyan motoci, ga iPhone, babu sauran wayewar da ta rage min -Gwanja

Karatun minti 1

Fitaccen mawaki kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Ado Isa Gwanja ya bayyana cewa babu wata sauran wayewa data rage masa a fadin duniya.

Rahoton DABO FM ya bayyana mawakin yayi wannan fariya ne a shafin sa na sada zumunta a safiyar Alhamis.

Gwanja ya bayyana cewa “Alhamdulillah, Nidai inaga ba wata sauran wayewa data rage min, babban gida, manyan motoci, kyakkyawar mata, diyata, babban studio, kudade a account, ga kuma iPhone 11 max pro.”

Wayar iPhone 11 max pro dai itace wayar da kusan tafi ko wace waya tsada gami da shahara a wannan zamani, inda kudinta ya gota rabin miliyan, domin tana kaiwa dubu 540 zuwa dubu 580.

Daga karshe Ado Gwanja ya karkare da cewa shifa ba gara bane kamar yadda wasu suke tinani, “Kuda kuke min kallon ban waye ba, menene ake kira da wayewa?”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog