INEC ta kwace ‘Certificate’ 20 na APC daga cikin jimillar 25 da aka kwace bisa umarnin Kotu

Karatun minti 1

Babbar hukumar zabe ta INEC ta kwace jimillar takardar shaidar lashe zabe ”Certificate of Return” guda 25, a zaben da aka kammala na 2019 bisa umarnin Kotunan zabe.

Shugaban sashin labarai da ilimin masu zabe na hukumar “IVEC”, Mr. Festus Okeye, shine ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki a fanni kafafen labarai na hukumar INEC wanda aka gudanar ranar Litinin a jihar Enugu.

DaboFM ta tattaro cewa; Mr. Okoye ya bayyana cewa, 20 daga cikin 25 da hukumar ta kwace, ta kwace su ne daga jami’iyyar APC ta kuma sake baiwa ‘yayan jami’iyyar APC, ta kwace 2 daga jami’iyyar PDP inda ta sake mayarwa da wasu ‘yayan PDP.

Jaridar Daily Trut ta rawaito Mr Okeye yana cewa; ”3 daga ciki, hukumar ta karba daga jami’iyyar APC da PDP ne inda ta baiwa wasu jami’iyyun.

“Kafin na baro shedikwatar INEC ranar Juma’a, hukumar ta kwace takardun shaidar cin zabe 25 daga wajen wadanda aka baiwa na ainahi zuwa ga wasu bisa umarnin Kotu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog