Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Kwanaki 131 tin bayan saka hannun shugaba Buhari akan dokar karin albashin N30,000

1 min read

A ranar Alhamis, 18 gawatan Afrilun 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu na aminta da karin biyan albashin ma’aikatan Najeriya daga N18,000 zuwa N30,000.

Har kawo yanzu dai karar kararrawar wayar ma’aikatan bata chanza salo ba, domin kuwa har zuwa yanzu babu batun biyan su kudin.

A cigaba da wasan ‘yar ganin laifi da akance gwamnatin shugaba Buhari ta kware a kai, gwamnatin dai ta bayyana cewa kungiyar kwadago ce ta hana a fara biyan albashin bisa wasu tsare-tsare na gwamnatin da kungiyar taki amincewa dashi.

DABO FM ta tattara cewa; zuwa yanzu dai , an shafe kwanaki kwanaki 131 daga ranar da shugaba Buhari ya sanya hannu da dokar.

Abin lura shine; Fadar gwamnatin tarayya ta bayyana dokar a matsayin wacce zata fara aiki nan take, sai dai har yanzu dokar bata kai ga taka kowa ba.

Gwamnatin jihar Kaduna kuwa, a ranar Litinin, 26 ga watan Agustan 2019, ya bayyana zata fara biyan ma’aikatanta sabon albashin daga watan Satumba bayan ta kori dubban ma’aikata a shekarar da ta shude.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.