/

Shekarau, Ahmed Lawan na daga cikin sanatoci 10 dake dumama kujera

Karatun minti 1
Shekarau
Mallam Ibrahim Shekarau - Sanatan Kano ta tsakiya (APC)

Shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawan, Adamu Bulkachuwa (APC, Bauchi) tare da tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Ibrahim Shekarau (APC, Kano) na cikin ‘yan majalisar da suka shekara guda cif ba tare da kai kuduri majalisar ba.

Rahoton DABO FM ya bayyana aikin dan majalisa na farko dai bai wuce kai kudiri ba, an rantsar da majalisar ta 9 ne a ranar 11 ga Yuni, an kuma kai kuduri fiya da 450 cikin shekara guda, kamar yadda wani kwarya-kwaryar bincike na DailyTrust ya tabbatar.

Ragowar sanatocin da suka kasa katabus a zauren majalisar sun hada da Christopher Stephen Ekpenyong (PDP, Akwa Ibom), Godiya Akwashiki (APC, Nasarawa), Emmanuel Yisa Orker-jev (PDP, Benue), Kabir Abdullahi Barkiya (APC, Katsina), Nicholas Olubukola Tofowomo (PDP, Ondo), Peter Onyeluka Nwaoboshi (PDP, Delta) da kuma Lawali Hassan Anka (PDP, Zamfara).

Da aka tuntubi Malam Shekarau akan wannan batu ya bayyana yanzu yana kan kokarin kai wani kudiri na gyaran dokar yan fansho.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog