/

‘Yan Sanda sun cafke Faston da ake zargi da sace Sadiya Idris tare da canza mata addini

Karatun minti 1

Rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna ta tabbatar da kamun wani malamin addinin Kiristanci, Pastor Jonah Gangas da ake zargi da sace wata yarinya ‘yar asalin jihar Kaduna.

Tin a ranar Laraba, DABO FM ta rawaici labarin yadda Fasto Jonah Gangas ya dauke Sadiya Idris tin a shekarar 2013, ya sauya mata addini ya kuma sanya ta a makarantar koyar da addinin Kiristanci a garin Jos na jihar Plateau.

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar, ASP MUhammad Jalge ya tabbatar da labarin inda ya shaida wa wakilin sashin Hausa na Legit cewa rundunar ta kama Faston da ake zargi tare da gufanar da shi a gaban Kotu.

“Mun samu rahotan bacewar Sadiya Idris shekaru 7 da suka wuce tin a watan Yuli, 2013. Bayan ta dawo gida ta bayyana ana cewar wani manomi ne ya tsince ta ya kuma kai ta wajen malamin coci.

“Da saninta ta karbi addinin kiristanci duk da cewa yardar ta ba ta da tasiri a lokacin saboda shekarunta 12 a wancen lokaci. Ta zauna tare da shi (Fasto), ya sanya a makaranta tin daga lokacin har zuwa dawowar a ranar Asabar (8/8/2020).”

“Malamin cocin yana hannunmu yanzu, mun kammala bincike kuma mun tura shi kotu.”

Rundunar ta bayyana cewa har yanzu dai kotu ba ta fara zama a kan shari’ar ba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog