/

Kwakwaf: Shin da gaske ne Najeriya ta fi kowace kasa kayan Noma a duniya?

dakikun karantawa

Shin da gaske ne kasaar Najeriya ta fi kowacce kasa a fadin duniya kayyakin Noma?

Al’umma da dama sun bayyana shakkunsu kan wasu bayanai da wani fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Dr Abdullah Gadon Kaya ya yi a kan auren wani matashi Sulaiman da amaryarsa Jenine yar kasar Amurka mai shekaru 45.

“Wace kasa ce za a gaya mana ta fi mu(Najeriya) Noma, ta fi mu kayan noma, kasar noma ko ta fi mu ruwa? a fada mana ko in da za a ce sun fi mu arzikin kasa.

DABO FM ta bibiyi batun domin gano hakikanin batun, haka abin yake ko kuma za a iya kiran maganar da zancen da aka takaita bincike wajen fadarsa ko ma wani abu akasin wadannan.

Duk da Najeriya kasa ce da ke cike da shugabannin da ake kallonsu maha’inta, za a yi mamaki a ce kasar da ta fi kowacce kasa kayyakin aikin noma ba ta iya samar wa kanta abinci da zai isheta har ma fitar zuwa kasashen da ta ke makwaftaka da su.

Shin Malamin yana nufin kyan kasa, kayyakin aiki na zamani da suka kunshi motocin tarakta da sauran abebaden aikin noman zamani, ko kuma yana nufin fin kowacce kasa a bangaren fitar da alfanun abin da aka shuka har duniya ta ke samu.

Za mu duba wadannan tambayoyi daki-daki mu kuma fitar da amsoshinsu.

A bangaren fitar da amfanin gona:

DABO FM za ta yi duba kan wani bincike da kamfanin Yahoo ya fitar ranar 16 ga Oktobar 2020 bisa madogarar wata kidudduga da bankin duniya ya yi a kan kasashen da duk duniya babu kamar su wajen fitar da amfanin gona. Yahoo ya fitar da jerin kasashe 25 da babu kamar su a wannan fannin duk fadin duniya.

Tin daga kasar farko har ta 25 babu kasar da ke Afrka ta yamma, kasar Afrika ta Kudu ce kadai a cikin jerin kasashen daga kafatanin nahiyar Afrika.

Kasashen su ne: China, Amurka, Turkiyya, Indiya, Brazil, Chile, Rasha, Iran, Ukraine, South Africa, Mexico, Japan, Australia, Peru, Argentina, New Zealand, Serbia, Canada.

Sauran sun hada da; Moldova, Belarus, Azerbaijan, South Korea, Kyrgyztan, da kuma Kazakhstan.

Rogo, Doya da Balili ne kadai Najeriya tafi kowa samarwa, sai Kubewa, Citta da Najeriya ta ke biye wa Indiya baya da kuma Dankalin Hausa da Najeriya take biye wa China baya, kamar yadda Kungiyar Noma da samar da abinci ta majalissar dinkin duniya FAOUN ta bayyana.

Bangaren kayyakin aiki na zamani:

Sanin kai ne cewa, alamu za su nuna cewa in da ake da masana’antun kira za su fi zama a kan gaba wajen yin kayan aikin zamani domin amfani a kasarsu. Kasar Najeriya ba ta cikin kasashe masu masana’antun kere-kere.

A watan Mayun 2020, gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ba wa manoma a jihar kyauta motar tan-tan guda 10 kacal , kamar yadda Jaridar Indepedent ta rawaito.

A kasar Indiya kadai, wakilinmu da ke zaune a can ya shaida mana cewar; “Wadatuwar tan-tan a Indiya ta kai ana yin dako da su, a sanya na’urorin sauti a yi ‘DJ’ a kauyuka.

Kasar Indiya ita ce kasar da ta fi ko ina samar da Tan-tan a duniya, kamar yadda yake a shafin Wikipedia.

Kasar Noma:

Mujallar Farm Progress ta kamfanin Informa na kasar Burtaniya ta rawaici cewa nahiyar North America ya fi ko ina kyan kasar noma a duniya in da gabashin Turai yake biye mata baya, tare da arewacin kasar China da yankin Argentina.

Bisa ga wadannan bayanai, ya nuna cewa ko alama, Najeriya ba ta cikin kasashen da a duniya suka yi fice wajen yin noma. Hatta a bangaren kiwo, samar da madara da nama, Najeriya ba ta jerin sama na wadanda suka fi kowa a duniya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog