/

Sadiya Idris: Yarinyar da Fasto ya boye tun tana shekaru 11 ya canja mata addini

dakikun karantawa

An samu nasarar chafke wani fasto mai suna Juna Gangas bayan ya boye yarinya, Sadiya Idris kimanin shekaru 7 a hannun sa tare da mayar da ita addinin kiristanci.

DABO FM ta tattara cewa yarinyar ta bace tun tana shekaru 11 a hannun kakarta a jihar Kaduna, basu kara saka ta a ido ba saida takai shekaru 19 da haihuwa.

Bayar bacewar ta, Sadiya ta bayyana cewa wani manomi ne ya dauke ta ya bawa wannan fasto bayan ta nemi taimako.

Bayan da fasto Juna ya karbeta yaki kaiwa jami’an tsaro rahoton batan nata inda yayi amfani da wannan dama da ya samu wajen sauya mata addini daga musulinci zuwa kiristanci.

Cikin wata hira da Legit TV mahaifiyar Sadiya ta bayyana cewa sun shiga tashin hankalin da har ta kai bakin ciki ya kashe mahaifin ta sakamakon ciwon hawan jini, haka kakarta ma irin wannan tashin hankalin ne ya yi sanadiyar mutuwar ta.

Jami’in kula da korafe korafe ta wata kungiyar kare hakkin bil’adama, Abubakar Awwal ya bayyana “Duk da cewa yarinyar ta tabbatar ba ayi mata fyade ko tirsawawa wajen cutar da lafiyar ta ba amma ba zamu bar abin ba har sai mun tabbatar an hukunta wannan fasto.”

“Kaduna gari ne mai matsalolin yare da addini mabanbanta idan dai ba’ayi hukunci ba Allah ne kadai yasan abinda zai afku.”

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya tabbatar mana da faruwar wannan aika aika, ya bayyana mana yanzu haka an shigar da maganar a kotu.

Hoto: Legit.ng

Karin Labarai

Sabbi daga Blog