(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Mai maganin gargajiya ya damfari wani dan Koriya ta Kudu miliyan 30 akan zai nemo masa lasisin NNPC

Karatun minti 1

Wani mai maganin gargajiya, Jamiu Isiaka, dan shekara 31, ya karbi laifin cutar wani dan kasar Koriya ta Kudu, Keun Sig Kim, kudi Naira Miliyan 30, domin nema masa lasisi a ma’aikayar mai ta Najeriya ‘NNPC.’

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC reshen jihar Ilorin, ta bayyana cewa; Isiaka ya badda kama inda yayi fitowa Keun Sig Kim a matsayin Daraktar ma’aikatar EFCC, Dr Maikanti da mai Magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina da sauran wasu manyan mutane a Najeriya.

Hukumar tace wanda take tuhuma tare da wasu mutanen shi sunyi amfani da sunan wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya wajen cutar dan kasar Koriya ta Kudu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa; Keun Sig Kim ta Kudu ya biya su Isiaku kudade kimanin Naira miliyan 30.

Kim ya bayyana cewa; “Na tura dala 4,285.071 zuwa bankin “UBA, mai lamba 2107575870 da sunan Jamiu Isiaka, mai aiki tare da Mr Shola Adeshina. An turomin wannan bayanan domin in tura kudade har sau 6.”

Isiaka ya karbi laifinshi inda ya bayyanawa EFCC cewa ya karbi kudin, sai dai yace yay i amfani da kudin ne wajen yiwa Mr Keun Sig Kim yanka domin ya samu lasisin.

Yace ya siyi Hanjin Giwa, Fatar Giwa, Kwakwalwar Zaki, Hantar Biri daga cikin abubuwan da zai sadaukar domin Mr Kim ya samu lasisin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog