Labarai

Gwamnonin Arewa suna tattaunawa kan shawo tsakanin Ganduje da Sarki Sunusi -Shatima

Gwamnan jihar Borno kuma tsohon shugaban kungiyar gwamnonin arewa, Kashim Shattima ya bayyana cewa suna tattauna kan sasanta abinda ke tsakanin gwamnan Kano, Dr Ganduje da Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II.

Shettiima ya bayyana haka ne yau Juma’a, a wajen taron gwamnonin Arewar da aka gudanar a jihar Kaduna.

Da yake magana da manema Labarai; Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa ;Duk da cewa wani gwamnan baya shiga hurumin abinda yake faruwar a jihar wani, amma dai wannan ya shafe su, musamman shi karan kanshi.

“Dukkanin su babu wanda bai yi mana abin yabawa ba, musamman mu a jihar Borno.”

“Ganduje ya dauki nauyin karatun marayu 200 da iftila’in Boko Haram ya rutsa dasu.”

“Ya hada da basu makwanci, yana ciyar dasu, a karatunsu tin daga matakin firamare har Sakandire.”

“Shima a nashi bangaren, Sarkin Kano, shine wanda yayi mana jan gora zuwa wajen Aliko Dangote. A shekarar 2016, Sarkin yazo da kafarshi har zuwa Borno domin yaga yacce aikin jinkan mutane yake tafiya.”

“Yayi magana da Aliko Dangote kuma wajen sau 3 Dangote yana zuwa Borno akan hakan.”

“Shine (Sunusi) wanda yafi kowa bamu gudunmawa a shirin mu na jinkai da ceton mutanen Borno wajen hada mu da wadanda suka bamu dauki sosai, bazan taba mantawa da Sarkin Kano ba.”

“Lokacin da yana bankin CBN, Sarkin ya dawo da cibiyar koyar da sana’o’i da kasuwanci zuwa jihar Borno a shekarar 2013.”

“Ya taimaka mana wajen wayar da kan al’ummar mu dama bayyanawa duniya irin halin da muka samu kanmu a jihar Borno. Bazan taba mantawa da Sarkin Kano ba, haka zalika shima Ganduje.”

Majiyoyin Dabo FM sun bayyana cewa Gwamna Kasshim yace sunada wani tsari da suke dashi na gwamnoni na cewa ba wanda zaiyi maka katsalandan wajen tafiyar da aikin jihar Ka, sai dai sukan yi duk mai yiyuwa wajen yin daben da za’a hau na tudun mun tsira.

“Inshaa Allah, Ganduje da Sarkin Kano zasu dawo tamkar tsintsiya mai madauri daya.

Dabo FM

Karin Labarai

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu-yanzu: Sarkin Karaye ya nada Kwankwaso Makaman Karaye kuma hakimi mai nada sarki

Muhammad Isma’il Makama

Muna aiki ta karkashin kasa domin sasanta Sarki Sanusi da Ganduje -Shekarau

Muhammad Isma’il Makama

Ganduje na shirin ayyana Sarkin Bichi a matsayin babban sarki a Kano

Muhammad Isma’il Makama

An shawo kan rashin jituwar Ganduje da Sarki Kano Sunusi

Dabo Online

Buhari ya kira Ganduje zuwa Abuja akan rikicinshi da Sarki Sunusi

Dabo Online

Yanzu- Yanzu: Masu zaben Sarki sun zauna don fidda sabon Sarkin Kano

Dabo Online
UA-131299779-2