Mata suna gane Namijin dake musu karya ‘Ido na Ganin Ido’ – Masana

Wata shiyar karatun Ilimin magani na Pharm D dake kasar Pakistan, tayi wani bincike akan kwakwalan mata da maza.

Binciken ya nuna wasu abubuwa da kwakwalan mata suka fi na maza, haka suma na mazan suka fi na matan a wani kaulin.

Ga jerin Binciken:

1. Yanayin aikace-aikace (Yin Aiki dayawa lokaci guda):

Mata: Kwakwalwar mata tana da karfin bada hankalinta akan abubuwa dayawa. Mata sukan iya “Kallon Talbiji a yayin da suke waya kuma suyi girki duk lokaci daya.”

Maza: Bisa tsarin kwakwalwar maza, tana mai da hankali ne akan abu guda daya a lokaci guda. Maza suna tsayar da Talbiji a lokacin da suke waya. Ma’ana bazasu iya yi lokaci guda ba.

2. Koyar Magana/ Iya sabon Yare:

Masu Alaƙa  Yin Tusa tsakanin Ma'aurata tana ƙara danƙon soyayya - Masana Lafiyar Jiki

Mata: Su na iya koyan yarurruka dayawa cikin ‘dan karamin lokaci. Saidai basa iya warware matsala a cikin sauki.

“Mata suna riga maza fara yin magana a lokacin da suke kanana. Mafi yawan lokaci yarinyar ‘yar shekara 3 tafi yaron shekarar uku magana da kuma sanin kalmomin yaren da suke yi.”

Maza: Maza basa iya yarurruka dayawa a cikin kankanin lokacin, hakan ya basu wuya. Saidai sukan shawo kan matsala cikin kankanin lokaci.

3. Yin Karya

Mafi yawan lokaci, mata sukan gane maza idan sukayi musu karyar ido na ganin ido, saboda kwakwalwar mata na da karfin gane maganganun fuska da kaso 70. Sai dai  kwakwalwar nada kashi 10 na gane karyar fatar baki, batare da an kalli juna ba.

Masu Alaƙa  Lemon Tsami yana kare jiki daga daukar cutar "Cancer", Daga Dr Guru Prasad

Matan sun kware wajen yin karyar ido na ganin ido.

4Yanayin Magana.

Mata: Kwakwalwar mata na amfani da hanyar lauye-lauye wajen yin magana. Ma’ana basa iya fadar magana kai tsaye ba tare da sun jinginata da wani abun daban ba.

Maza: Kwakwalwar maza na kaisu ga fadin magana kai tsaye bisa abinda zuciyarsu take nufi.

5. Magance motsin Rai/Zuciya

Mata: Sukayi magana mai yawa a lokaci daya ba tare da dogon tunani ba.

Maza: Sunayin tunani sosai kafin furta kalamai.

6Abinda kowa yafi so.

Maza: Maza suna son girma da daukaka tare da jin dadin warware matsaloli.

Masu Alaƙa  Mata masu tabin hankali a Najeriya sunfi 'yan kasar Canada, Morocco da Andalus yawa

Mata: Kyakkyawar dangantaka, nuna kulawa ‘yan uwa hadi da son hira.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: