Mahaifin Kakakin Majalissar Jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum ya rasu

Allah ya yiwa Mahaifin kakakin majalisar jihar Kano, Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum rasuwa.

Gidan Talabijin dake jihar Kano na ARTV (Mai Asin da Asin), ya rawaito a labaran karfe 12 da suke cikin harshen Hausa a yau Alhamis.

Wasu daga cikin al’ummar jihar Kano, sun kai ziyarar ta’aziyyar su ga Hon Kabiru Rurum.

Daga cikin wadanda suka halarta sun hada da, Wamban Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Hakimin Karamar hukumar Bunkure, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo.

Wakilai daga wasu manyan gidajen rediyo dake fadin Kano da Kano dama wasu daga cikin zabbabbun ‘yan Majalissun wakilai na jihar Kano da ketare.

Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum wanda yanzu shine zababben dan majalissa da zai wakilinci karamar hukumar Rano dake jihar Kano.

%d bloggers like this: