Home SharhiMe gwamnatin tarayya take nufi da dora hoton Sarkin Kano da Buhari kadai? Ba Ganduje da Sarakuna 4

Me gwamnatin tarayya take nufi da dora hoton Sarkin Kano da Buhari kadai? Ba Ganduje da Sarakuna 4

by Dabo Online
0 comments

Bayan kammala taron yaye daliban makarantar koyar da aikin dan sanda dake jihar Kano, fadar Gwamnatin Najeriya ta wallafa hotunan zuwan da shugaba Buhari yayi a shafinta na Twitter @NigeriaGov.

Sai dai wallafa hoton ya janyo cece-kuce bisa dalilin rashin sanya hoton Ganduje da sauran sabbin Sarakunan Kano guda 4.

An dai hangi Shugaba Muhammadu Buhari yana gaisawa da Sarkin Kano Muhammadu Buhari, hotunan ‘yan sandan da aka yaye tare da lokacin da ake yiwa shugaban fareti.

DABO FM ta tattara cewa hatta hoton babban Sifeton ‘yan sandan kasa, fadar shugaban bata daura ba.

Ko me hakan yake nufi?

Zaku iya bayyana ra’ayiyinku a shafinmu na Facebook a Dabo FM

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00