//

Abubuwan da zasu iya faru wa in Sarki Sunusi ya ketare wa’adin Ganduje

0

Biyon bayan wa’adin kwana biyu da gwamnan Kano ya baiwa Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, na karba ko barranta daga shugabancin da aka nadashi, DABO FM ta tattara abubuwan da ka iya faruwa.

Bisa ga sabuwar dokar Majalisar Sarakunan jihar Kano, ta gindaya sharadin tare da hukuncin duk wanda yaki biyayya ga umarnin gwamna.

Dokar ta kuma bawa gwamna umarnin tsige dukkanin wani Sarki da ya ketare umarninshi ko ya saba wata doka dake kare Majalissar.

DABO FM ta tattaro, duk dai a dokar, idan Sarki yaki halartar taron majalisar har guda 3, gwamna yana da damar da zai cire shi.

Masu Alaƙa  Hukumar yaki da Cin hanci ta jihar Kano ta bukaci a dakatar da Sarki Sunusi

Ko Ganduje zai yi amfani da dokar da ya bawa kanshi wajen tsige Sarki Sunusi?

Ga duk wanda yake bibiyar takaddamar dake tsakanin masu mulkin biyu, to ba shakka zai bayar da amsar cewa “Lallai zai tsige shi.”

Alamu sun nuna soyuwar gwamnatin Kano akan yin duk mai yiwuwa wajen tsige Sarkin, wanda tin a farko gwamnatin tayi ta neman hanyar sauke Sarki cikin sauki. Tin daga kan zarginshi da yin almundahana da kuma zargin goyon bayan jami’iyyar PDP a zaben gwamna, alkaluma sun nuna gwamnatin na son tsigeshi.

Ganduje yana da damar tsige Sarki Muhammadu Sunusi II, ta hanyar amfani da hukuncin hukunta duk wanda ya karya dokar Majalissar idan har wa’adin da aka bashi ya shige bai yi yacce gwamnan yake so ba.

Masu Alaƙa  Rikicin Kano zai iya shafar Masarautun Arewa - Attahir Bafarawa

Haka zalika, yana iya sauke shi daga mukamin shugaban Majalissar zuwa komawa dan Majalissar ba tare da wani mukami ba.

Sai dai gwamnatin Kano tana tsoron tashin hankali da ka iya faruwa a dalilin cire Sarkin duba da yacce mutane suke kaunarshi a yanzu. Wannan yana daga cikin dalilin da yasa gwamnatin ta kasa budar ido tace ta tsigeshi tin da farko.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020