//
Wednesday, April 1

Iyalan Marigayi Ado Bayero da Mal Shekarau zasu nemi hakkokinsu na sharrin kisan Sheikh Jafar?

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A daidai lokacin da malamai da al’umma suka gaskata ikirarin kisan Sheikh Jaafar da Boko Haram ta ayyana aiwatarwa, DABO FM ta tattaro batutuwan zarge-zarge da akayi kan masu hannu a kisan malamin.

Mai martaba Sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero, Mallam Ibrahim Shekarau da Danjuma Goje suna daga cikin manyan da aka zarga da kisan fitaccen malamin. Da Ado Muhammad na gidan rediyon Freedom.

Idan ba’a manta ba a watan Afirilun shekarar 2017, yan sandan Najeriya sun kai sumamen bazata zuwa gidan Sanata Danjuma Goje inda suka dauke kudade kimanin Naira miliyan 18, Dalar Amurka dubu 19 da Riyal dubu 4 tare da fayil-fayil na kasafin kudin Najeriya.

Masu Alaƙa  Adadin ‘yan Najeriya dake son satar kudin kasa yafi na wadanda suka sace da masu sata a yanzu

Rundunar tace “Ta samu fayel da ya nuna bayanai kan yadda tsohon gwamnan Kano, Mallam Shekarau, ya kitsa hallaka Sheikh Jaafar Kano” kamar yadda mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Jimo ya bayyana. Lamarin da Goje ya karyata wanda itama rundunar bata kara magana akan batun ba.

Haka zalika, a ranar 30 ga watan Satumbar 2009, Sahara Reporters, ta wallafa rahoton tabbacin da a cewarta “Mallam Shekarau, Marigayi Ado Bayero suna da hannu a cikin kisan Sheikh Jaafar.”

Sahara Reporters ta zargi kafafen laabaran Arewa ta kin yada binciken da suka gudanar akan kisan malamin bisa karbar makudan kudade daga gwamnatin jihar Kano.

Masu Alaƙa  Labaran Karya: Auren Shugaba Buhari da Sadiya Faruk ba gaskiya bane

Itama DABO FM ta kawo batun Sahara Reporters don kaucewa kage da samun tushen mai karantu.

Jaridar ta bayyana karara cewa “Shekaru ne ya kashe Jaafar a lokacin mulkinshi tare da samun goyon bayan Sarkin Kano, marigayi Dr Ado Bayero.”

Bayan wani faifan bidiyo da shugaban yan ta’adda na Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar, yayi nuni da cewa kungiyar ta dauki alhakin kisan fitaccen malamin wanda malamai irinsu Sheikh Abdulwahab suka gaskata.

Idan ta tabbata mayakan ne suka kashe Malamin, lallai ya tabbata Sahara Reporters tayi wa Shekaru da Marigayi Ado Bayero karya wanda hakan ya saba da dokar Najeriya, duk da cewa tin a wancen lokacin, mutane basu gaskata ikirarin jaridar ba.

Masu Alaƙa  Adadin ‘yan Najeriya dake son satar kudin kasa yafi na wadanda suka sace da masu sata a yanzu

Shin kuna gani lokaci yayi da iyalan marigayi Ado Bayero da Mallam Shekarau zasu dauki matakin shari’a akan sharrin da jaridar tayi musu?

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020