Bincike Labarai Ra'ayoyi

Adadin ‘yan Najeriya dake son satar kudin kasa yafi na wadanda suka sace da masu sata a yanzu

Shuwagabannin Najeriya, sun kasancewa daga cikin shuwagabanni mafi zarra a wajen yi wa asusun kasa ta’annati a fadin duniya.

Satar miliyoyin kudade ya zama tamkar wutar lantarki a kasashen turai domin a kowanne matakin gwamnatin wanda ya hada da tarayya har zuwa karamar hukumar, ana samun masu handame kudaden da ba halaliyarsu ba.

Haka zalika a bangaren da sha’anin mulki ba, duk wata ma’aikata da kudade sukan gifta, ana samun handame kudin komin kankanta da yawanshi.

Duk da cewa gwamnati mai ci a halin yanzu tace tana kokarin yaki da masu satar kudin kasar wanda dole ne a yaba mata bisa irin kokarin da takeyi.

Sai dai ba anan gizo ke sakar ba, domin adadin masu son sace kudin kasar, sunyi adadin wadanda suka taba satar kudi a Najeriya.

Zaku yarda dani cewar adadin masu son satar sunfi yawa idan ku da kanku kuka gudanar da bincike a tsakan-kanin inda kuke rayuwa.

Ku lura a duk lokacin da ake maganar shuwagabanni masu satar dukiyar al’umma, dayawa daga cikin matasan da suke wajen suna furta kalmar “Barsu suyi ta diba, muma Allah Ya kaimu wajen mu kwashi rabonmu kawai.”

Ina batun gyara a al’ummar da matasanta suke fadar irin wannan kalaman? Ya kuke gani idan wadannan suka dare kan karagar mulki?

‘Ba shakka satar biliyan 10-40 zata zama ba komai ba.’

Sanin kowa ne matasa sune ginshikin cigaban kowacce al’umma musamman a kasa irin Najeriya wacce fiye da kaso 60 na mutanen kasar Matasa ne.

Bawa matasan Najeriya Ilimi da kuma sanya musu kishin kasa ne kadai zai iya fidda kasar daga wannan kangin ta take hanyar shiga.

Allah Ya kyauta.

Karin Labarai

Masu Alaka

Iyalan Marigayi Ado Bayero da Mal Shekarau zasu nemi hakkokinsu na sharrin kisan Sheikh Jafar?

Dabo Online

Labaran Karya: Auren Shugaba Buhari da Sadiya Faruk ba gaskiya bane

Dabo Online
UA-131299779-2