Labarai Sharhi

Kalaman Sheikh Daurawa sun janyo cece-kuce tsakanin magoya bayan gwamnatin Kano

Kalaman Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa akan dambarwar dake tsakanin gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Mal. Muhammadu Sunusi II, ya janyo cece-kuce.

Sheikh Daurawa, a hudubar da ya gabatar a jiya Juma’a, yace ‘yan majalissu suyi doka kan ladabtar da masu batanci ga shugaba SAW tare da jan hankali da su maida hankalinsu wajen kawo wa al’ummar Kano mafita akan al’amuran da suka kamace su ba zancen tuhume-tuhumen Sarkin na Kano ba.

Malamin yace idan suna son cire Sarki, su cire shi kai tsaye ba tare da yin abu irin na raina tunanin al’ummar jihar da suke bukatar tsaro, ilimi, ruwan sha da sauran ababen tafiyar da rayuwa.

“Kuyi mana dokar da zata hana cin mutunci ga Manzon Allah SAW. Dan siyasa, Malami ko dan wata kungiya, idan ya fadi maganar da ake jin akwai rashin ladabi, a kirashi gaban kwamiti a ladaftar dashi.

Amma kun (‘Yan majalissa) shagala da yin doka kan Sarki, ina ruwanmu da maganar sarki, idan bakwa sonshi ku tsigeshi mana.”

“An shiga rana, an sha wahala an zabeku, wasu sun mutu, sun rasa dukiya, anyi sare-sare don kuje majalissa kuyi aiki.”

“Kwanannan aka zagi annabi SAW, aka kai hari Bagwai, Bichi, amma kuna ta maganar Sarki, kun maida abin ‘Drama’.”

Sai dai hudubar malamin bata yi wa wasu daga cikin magoya bayan gwamnatin Kano dadi ba musamman a zargin da sukace suna yi wa malamin na goyon bayan tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.

DABO FM ta tattara cewar a makon da muke ciki ne yan majalissar Kano suka bukaci Sarkin Kano ya hallara a gabanta domin amsa tambayoyi bayan korafi da majalissar tace an shigar gabanta game da wasu dabi’u da halayen Sarkin na Kano.

Daga bangaren al’ummar unguwar Ja’en da majalissar tace dan unguwar ne ya kai musu korafin, sun barranta da ikirarin majalissar har ma sun mika majalissar zuwa gaban kotu domin ta fitar da sunayen wadanda suka kai korafin.

Alakar gwamnatin Kano da Masarautar Kano ta kara tsamari ne yayin gudanar da zaben gwamnan jihar Kano a watan Maris na 2019 inda gwamnatin jihar ta zargi Sarki Muhammadu Sunusi II da goyon bayan dan takarar gwamnan PDP, Abba Kabir Yusuf, a zaben 2019.

Hakan ya janyo rarraba masarautar Kano zuwa gidaje 4 wadanda suka hada da Bichi, Rano, Gaya da Karaye.

Masu Alaka

Yanzu-yanzu: Sarkin Karaye ya nada Kwankwaso Makaman Karaye kuma hakimi mai nada sarki

Muhammad Isma’il Makama

Muna aiki ta karkashin kasa domin sasanta Sarki Sanusi da Ganduje -Shekarau

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2