//

Sarakunan Kano guda 5 basu gaisa da juna ba a taron da ya tilasta haduwarsu gaba daya

0

Sarakunan dake karkashin Majalissar Sarakunan ta Kano, sun hadu a wajen taron yaye daliban makarantar koyar da aikin dan sanda da take garin Wudil a jihar Kano.

Taron dai ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamna Ganduje, baban sifeton ‘yan sanda na kasa da sauran manyan mutanen dake ko ina a fadin tarayyar Najeriya.

Sai dai abin lura, wanda jaridar Daily Nigerian ta bincika, rashin gaisawa tsakanin sabbin Sarakunan jihar guda 4 tare da Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II.

Daily Nigerian, wacce wakilinta ya samu halartar taron ta bayyana yacce aka nuna babu sani ba sabo a tsakanin sarakunan da Sarkin na Kano.

”Duk da cewa Sarkin Kano, Sunusi, shine yazo daga karshe, bai gaishe da sauran Sarakunan ba, haka zalika suma basu gaishe dashi ba.”

Masu Alaƙa  Ganduje ya turawa Sarki Sunusi takardar tuhuma kafin a dakatar da shi

DABO FM ta tattaro cewa an ware wajen zaman Sarakunan su 5 duk a waje daya. Sai dai bayan zuwan Sarkin na Kano, aka chanza gurin da zai zauna zuwa wajen da aka warewa Sarkin Kuje na tarayyar Abuja.

Da yake bayyana dalilin rashin gaisawar, daga cikin masu yi wa Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa “Lokacin da ya iso, shi ma bai gashe dasu ba.”

Suma a nasu bangaren, daga cikin masu yi wa Sarkin Kano Sunusi hiduma, ya bayyana cewar; “Bamu damu dan basu zo sun gaishe da Sarkinmu ba.”

“Tinda dai Sarkinmu ya nemi waje ya zauna a kujerashi, bamu damu da girmamawarsu ba.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020