Labarai Sharhi

Ko yaya tasirin hudubar Sheikh Daurawa akan tsige Sarkin Kano?

A ranar Juma’ar da ta gabata, daya daga cikin malaman jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, yayi huduba akan dambarwar dake tsakanin Gwamnatin da Majalissar Dokokin jihar Kano da Sarkin mai murabus, Muhammadu Sunusi II.

An jiyo malamin yana magana mai dauke da kamar shawara da nusarwa zuwa ga bangarorin da suyi abinda zai amfani mutanen jihar Kano ba rigimar dake tsakaninsu ba, har ma yayi kira ga majalissar data kirkiri dokar da zata bayar da damar hukunta masu cin mutunci da zagin janibin Annabin tsira, Muhammad SAW.

Haka zalika ya shawarci gwamnatin da ta dena wasa da hankalin al’ummar jihar, yana mai cewa; “Idan bakwa sonshi, ku cireshi mana, ina ruwanmu da maganar Sarki.”

Kalaman malamin da wasu musamman masu goyon bayan gwamnatin jihar basu ji dadin kalaman ba har ma suke sukar malamin kan cewar dama shi ya dauki bangaren goyon bayan tsohon gwamnan jihar Engr Rabi’u Musa Kwankwaso wanda dama gwamnatin tana zargin Sarki mai murabus da goyawa dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf baya a zaben 2019.

DABO FM ta tattara cewar, kwanaki biyu da yin hudubar, gwamnatin jihar Kano ta hannun sakatarenta, Alhaji Usman Alhaji, ta bayyana tsige Sarkin a ranar Litinin.

Shin ko gwamnatin ta karbi shawarar malamin? Ko kuma ta aiwatar da shirinta da ta kudirin niyyar aikatawa tin fari?

Zaku iya bayyana ra’ayoyikin a kan shafukanmu na sada zumunta.

UA-131299779-2