(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

‘Mijinta ne yayi mata dukan tsiya ya caka wa kanshi wukar’ – Waye me gaskiya tsakanin dangin miji da matar?

dakikun karantawa

Tin bayan bayyanar faruwar wannan lamari ake ta samun rahotanni daban daban.

Sai dai yayin binciken mu a nan DABO FM mun tattaro wasu bayanai daga majiyoyi guda hudu.

DABO FM tattaro rahota daga bangaren dangin Sa’eed Muhammad, angon Fatima Hanan, sun bayyana cewa uwargidanshi ce ta caccaka masa wuka a daren Juma’a, 22 ga watan Yulin 2019.

Bangaren dangin Fatima Musa, bayan mun tattaunawa da wata daga cikin danginta sun bayyana cewa hatsari Sa’eed Muhammadu yayi a daren jiya Juma’a.

Sai dai wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan Instagram da cewa Sa’eed ne ya sheka wa Fatima Musa dukan kawo wuka, lamari daya faffasa mata jiki tare da kumbura mata fuska.

Rahotan dai yace Sa’eed ne da kanshi ya lumawa kanshi wuka domin kaucewa daga karbar hukuncin dukan mata da doka ta haramta.

Binciken namu ya cigaba inda muka tattauna ta wayar tarho da wasu daga cikin kawayen Fatima, ma’ana abokan karatunta na jami’ar Bayero inda take karantar ‘Law’.

DABO FM ta tattauna ta wayar tarho da wasu daga cikin abokan karatun ta wacce ta bukaci mu sakaya sunanta inda ta bayyana mana kadan daga cikin abinda ta sani game da batun.

“Hanan kawar muce tin muna aji daya a BUK, mace ta nitsattsiya mai dattaku.”

Ta bayyana mana cewa tana ganin auren dole ne ya janyo ta aikata wannan mummunan aikin inda ta tabbatar da cewa wanda Fatima take so bashi aka aura mata ba.

“Duk munsan saurayinta, wani dan Katsina sunanshi Ahmad amma lokaci daya mukaji za’ayi bikinta da Sa’eed bayan haduwarsu a kasa da wata 1.”

“Bamu san ma anyi bikinta ba, sai ji kawai mukayi ance ai Fatima tayi aure.”

Yanzu dai Fatima Musa tana hannun ‘yan sanda a tsare.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog