Labarai

Anyiwa Fatima Musa aure da Sa’eed a watan farko na haduwarsu bayan an rabata da wanda take so

Auren dole ne yasa Fatima Musa ta caccaka wa mijinta wuka bayan haduwarsu da wata 1 kacal

Bayan bincike da DABO FM ta gudanar, mun gano makasudin yunkurin da Fatima Musa takeyi na ganin ta kashe mijinta.

Fatima Musa Hamza dai dalibace da take karatun Law a jami’ar Bayero dake jihar Kano.

DABO FM ta tattauna ta wayar tarho da wasu daga cikin abokan karatun ta wacce ta bukaci mu sakaya sunanta inda ta bayyana mana kadan daga cikin abinda ta sani game da batun.

“Hanan kawar muce tin muna aji daya a BUK, mace ta nitsattsiya mai dattaku.”

Ta bayyana mana cewa tana ganin auren dole ne ya janyo ta aikata wannan mummunan aikin inda ta tabbatar da cewa wanda Fatima take so bashi aka aura mata ba.

“Duk munsan saurayinta, wani dan Katsina sunanshi Ahmad amma lokaci daya mukaji za’ayi bikinta da Sa’eed bayan haduwarsu a kasa da wata 1.”

“Bamu san ma anyi bikinta ba, sai ji kawai mukayi ance ai Fatima tayi aure.”

Yanzu haka dai Fatima tana tsare a hannun rundunar ‘yan sandan jihar Kano.

Sai dai bayan tattaunawa da wasu daga cikin bangaren dangin Fatima Musa, sun shaidawa DABO FM cewa hatsari ne ya rutsa dashi kuma babu zancen Fatima ta caccaka masa wuka.

Inda a daya bangaren kuma, bidiyo da yake ta yawo a shafukan sada zumunta, wasu na ganin mijin ne ya dake ta wanda har ya yayyaga mata kaya tare da kumbura mata wasu sassan jikinta.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kano: Budurwa ‘yar shekara 17 ta kashe kanta saboda mahaifinta ya saki mahaifiyar ta

Dabo Online

Amarya ta caccaka wa mijinta wuka a karo na 3 da take yunkurin kashe shi

Dabo Online

‘Mijinta ne yayi mata dukan tsiya ya caka wa kanshi wukar’ – Waye me gaskiya tsakanin dangin miji da matar?

Dabo Online

Matar da ta kwararawa Mijinta tafasasshen ruwan zafi ta tsere zuwa jihar Jigawa – ‘Yan Sanda

Dabo Online

‘Yan sandan jihar Jigawa sun cafke Matar da ta watsa wa Mijinta ruwan zafi a al’aurarshi

Dabo Online

Kotu ta bayar da belin Matar da ake zargi da caccakawa Mijinta wuka

Dabo Online
UA-131299779-2