Labarai

Hukumar Alhazai ta rage kudin aikin Hajjin 2019 tare da kara wa’adin biyan kudi

Hukumar aiki Hajji ta kasa Najeriya NAHCON, ta rage kudin aikin hajjin shekarar 2019 bayan wata ‘yar bita data gudanar game da kudaden.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun mai hulda da jama’arta, Fatima Sanda Usara, a daren ranar Asabar.

Hukumar tace an samu ragin kudaden ne bayan wata ganawa da tayi tare da sauye sauyen hanyoyin sufurin da mahajjata zasu bi tare da rage kudaden da ma’aikatar sufurin kasar Saudiyya tayi.

Hukumar tace an samu ragin Riyal 620 kusan dalar Amurka 165 daga kudin da hukumar ta ayyana a farko na kowacce jiha hadi dana jami’an tsaro.

Sanarwar tace alhazan jihohin Najeriya da babban birnin Abuja da jami’an tsaro sun samu ragin Naira 51,170.45 daga cikin kudin farko da hukumar ta fitar a makonnin da suka gabata.

Hukumar ta bawa dukkanin hukumomin dake jihohin Najeriya baki daya dasu bada sanarwar ragin kudin da karin wa’adin aikin hajjin na shekarar 2019.

Haka zalika hukumar ta kara wa’adin rufe biyan kudin aikin hajjin har zuwa 15 ga watan Julin 2019 bayan karbar bukatar da aka shigar gabanta na neman karin wa’adin.

NAHCON tayi kira ga masu niyar halartar aikin hajjin dasu tabbatar da sun gama biyan dukkanin wasu kudaden da zasu biya da kuma fara shirye-shiryen tafiya.

Karin Labarai

Masu Alaka

Hajj2019: Kada jama’a su yadda da kudin aikin Hajjin 2019 da ake turawa a Social Media – Hukumar Alhazai

Dabo Online

‘Yan Najeriya 65,000 zasu yi aikin Hajjin 2019, adadin da ya ragu da 10,000 a shekarar 2014

Dabo Online

‘Yan Najeriya 65,000 ne sukayi aikin Hajjin Bana – Hukumar Alhazai

Dabo Online

Kaduna,Abuja: Kudin aikin Hajji na bana, Naira miliyan 1.5 – Hukumar Alhazai

Dabo Online

An samu ragin N51,170 daga cikin Naira miliyan 1.5 na kudin aikin Hajjin 2019 – NAHCON

Dabo Online
UA-131299779-2