//
Tuesday, April 7

Dole ku sanya yaranku a makarantun gwamnati – El-Rufai ga jami’an gwamnatin Kaduna

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a fadar shugaban kasa Abuja inda yace: “Mun bada umurninn cewa ya zama wajibi dukkan ma’aikatan ma’aikatar ilmin jihar Kaduna da ke da hakkin inganta ilimin yaranmu su sanya yaransu a makarantar gwamnati.”

Makonni biyu bayan kai yaronsa, gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa ya laburtawa dukkan ma’aikatan bangaren ilimin jihar Kaduna cewa ya zama wajibi su kai yaransu makarantun gwamnatin jihar.

Kamar yadda yayi alkawari a shekaru biyu da suka gabata, gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa’i, ya shigar da yaronsa, Abubakar Al-Siddique El Rufa’i, makarantar gwamnatin Kaduna Capital School dake unguwar Malali Kaduna. A ranar Litinin, 23 ga watan Satumba, Gwamnan tare da amaryarsa sun kai Abubakar mai shekaru 6 da haihuwa makarantar inda zai yi karatun firamarensa.

Masu Alaƙa  Zaben Gwamna: El-Rufa'i na jami'iyyar APC ya lashe zaben gwamnan Kaduna karo na biyu

Hakazalika Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa ba zai cire yaronsa, Abubakar El-Rufa’i, daga makarantar gwamnati ba duk da garkuwa da mutanen da akayi da daliban wata makaranta a jihar jiya.

“A kan al’amarin kai yarona makarantan gwamnati kuma, wannan alkawari ne na cika kuma hakan ya bayyana cewa na yi imani da ingancin makarantun gwamnati tun da yarona na zuwa.”

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020