//
Tuesday, April 7

Zamu zama tsani tsakanin masu mulki da wandanda ake mulka – Majalisar Matasan Najeriya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Zariya, Nijeriya.

A cigaba da zagayen da take domin ganawa da kungiyoyi masu zaman kansu, a Asabar din da ta gabata, Majalisar Matasan Nijeriya reshen karakar hukumar Zariya, ta cigaba da ganawa da wakilan daukacin kungiyoyi masu rajista na gundumar Tudun Wada.

Taron da DABO FM ta halarta, ya maida hankali ne ga batun gabatar da korafe-korafe da muhinman matsalolin da suke damun yankin.

Da yake jawabin bude taron, shugaban kungiyar Kwamared Usman Hayatu Mazadu, wanda mataimakin sa Kwamared Bashir Yunusa, ya wakilta ya bayyana cewa; a kowanne zama irin wannan, sukan maida hankali ne ga karbar korafe-korafe da zummar gabatar da shi ga mataki na gaba, wanda kuma hakan ne ta sanya suke a Gundumar Tudun Wada a wannan makon.

Masu Alaƙa  Ko Sarkin Kano da Ganduje sun shirya ya kamata a kammala bincike - Barr Abba Hikima

Ya kara da cewa, kadan daga cikin manufofin Majalisar Matasa, shi ne, zama tsani tsakanin masu mulki da wanda ake mulka.

A saboda haka ne ma suke iya bakin kokarin su a koda yaushe, domin sauke nauyin da ya rataya a kansu.

Ya bada misalin wasu nasarorin da suka samu saboda gudanar da irin wannan bibiyan, da ya hada da sanadiyar gyaran gadan dake sabuwar hanyar Jos dake a Galma Zariya, sai naimo karin kudin harkokin gudanarwa na Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zariya.

A nashi jawabin, Sakataren yada labarai da hulda da Jama’a na Majalisar, Kwamared Umar Abubakar, ya yi bayani ne a kan halin da kungiyoyi ke ciki a karamar hukumar Zariya, wanda ya nuna damuwar sa bisa cewar, a kaf fadin gundumar Tudun Wada, kungiyoyin da suke da rajista a Gundumar basu wuce guda Talatin ba, wanda ya nuna fatan samun sauki daga lokacin da aka gudanar da wannan taron.

Masu Alaƙa  Taskar Matasa: Abbas Nabayi, matashi mai zanen da yafi hoton kyamara

Daya daga cikin mahalarta taron, kuma Shugaban Kungiyar Arewa Multi-purpose Training, Muhammad Nura Shitu Musa, ya nuna damuwar sa akan rashin Makarantar Babban Sakandare, wato Senior Secondary School, fadin Gundumar Tudun Wada, wanda Kuma ya ce, hakan na tauye Ilimi yara masu tasowa matuka.

Sai dai ya naimi al’umma, su dauki ragamar gudanar da aikin gayya domin rage ma gwamnati wasu nauyi da ya rataya a kan ta.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020