Labarai

Gwamna Fayemi na jihar Ekiti ya tabbatar da fara biyan albashin N30,000 daga watan Oktoba

Governor Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Dakta Fayode Fayemi, ya bayyana cewa gwamnatinshi zata fara biyan ma’aikatan jihar sabon albashin N30,000 daga watan Oktobar 2019.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin taron ranar Malamai ta duniya da aka gudanar a garin Ado-Ekiti, babban birnin jihar.

Gidan Talabijin na Channels ta rawaito gwamnan yana cewa; “Gwamnati ta kammala shirinta na fara biyan mafi karanci albashi na N30,000 daga wannan watan (Oktoba).

Furucin gwamnan yayi matukar farantawa malaman dake filin taron rai inda suka shiga cikin mamaki tare da yin murna da farinciki. – Channels ta tabbatar.

Zuwa yanzu dai jihohin Kaduna da Kebbi sun karbi sabon Albashin tin a watan Satumbar data gabata.

Inda a yau, Asabar, 5 ga Oktoba, shima gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ya alkauranta biyan sabon albashin.