Najeriya tana da masu tabin hankali miliyan 60 – Ma’aikatar Lafiya

“Ciwon Hauka a Najeriya yana karuwa sosai. Mutane suna kara samun tabin hankali bisa wahalhalun da ake fama dashi a kasar nan. Basu da kudi, mutane da dama suna fadawa shan magani ba tare da umarnin masana na ba. Mutane dayawa suna yiwa giya shan ganganci da ta’ammali da miyagun kwayoyi irinsu Tramol da tabar wiwi.

Daga bakin kwararren likitan kwakwalwa na Asibitin Koyarwa na jami’ar Ilorin, Dr Baba Issa.

Binciken da muka gudanar a nan DaboFM, mun binciko wata kiddidiga da ma’akatar kula da lafiya ta Najeriya fitar tare da kokenta akan lamarin.
Hukumar kula da lafiyar tace kashi 30 daga cikin 100 na adadin mutanen Najeriya suna da tabin hankali.

Masu Alaƙa  Lemon Tsami yana kare jiki daga daukar cutar "Cancer", Daga Dr Guru Prasad


Su ma a nasu bangaren masana kiwon lafiya sun tabbatar da hakan tare da cewa damuwa, tsanani, kunci da wahalar rayuwa, yana daga cikin abinda yake janyowa kasar yawan masu tabin hankalin.

DaboFM ta binciko cewa daga cikin adadin ‘yan Najeriya miliyan 201, mutane 60,300,000 ne suke da tabin hankalin. Sune kaso 30 na adadin ‘yan Najeriya.


Adadin yawan da Najeriya take su da masu tabin hankali yanada matukar yawa, hakan yasa muka sake binciko wasu kasashe da adadin masu tabin hankali a Najeriya yafi yawan adadin mutane dake rayuwa a kasashen.


Ga jerin wasu daga cikin manyan kasashen duniya da masu tabin hankalin Najeriya sukafi kasar yawa;

Masu Alaƙa  Cin Nama yana kara yawaitar wari a jikin 'Dan Adam - Masana


Canada tanada mutane miliyan 36, Spaniya, miliyan 46, Morocco, Miliyan 35, Ghana, miliyan 28, da kasar Holland mai mutane miliyan 17.

Bisa binciken da Dr Auwal Sani Salihu na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake jihar Kano ya gudanar, Dr Auwal yace kaso 6 daga cikin 10 na matan Najeriya suna da tabin hankali, inda suk kuma maza suke da kaso 4.


Daga cikin adadin 60,300,000 na masu tabin hankalin na Najeriya, 36,180,000 daga cikinsu Mata ne, 24,120,000 Maza.

Mata suke da kaso 18, Maza kuma nada 12 daga cikin kaso 30 na ‘yan Najeriya masu tabin hankali.

Gargadi

Ba’a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta “submit@dabofm.com

Sako na musamman

Masu Alaƙa  Mata masu tabin hankali a Najeriya sunfi 'yan kasar Canada, Morocco da Andalus yawa

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: