Sanatoci sun aminta da kudirin Shehu Sani akan mayar da Kadpoly zuwa Babbar Jami’ar Fasaha

Karatun minti 1


Majalissar dattawan Najeriya ta 8, ta aminta da kudirin mayar da Kaduna State Polythecnic zuwa babbar Jami’ar Fasaha bayan karatu na uku akan kudirinn.


Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin da Sanata Barau Jibrin (APC, Kano) yake jagoranta na makarantun gaba da sakandire ya gama tattara bayanshi a gaban majalissar

DaboFM ta hada bayanan da suka tabbatar da cewa; Sanata Shehu Sani na jihar Kaduna ne ya fara shigar da kudirin wanda ya samu aminta bayan karatu na 3 daga dukannin sanataoci a zaman da sukayi jiya.

Ana saka ran majalissar dattawan zata aike da kudirin zuwa majalissar wakilai da gaggauwa har zuwa aike shi ga shugaba Muhammadu Buhari kafin wa’adin majalissar ya kare a 9 ga watan Yuli.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog