Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Buhari zai gina sabon dakin saukar fasinjojin jiragen sama a jihar Legas akan Naira Biliyan 14 – Minista

2 min read

Ministan harkokin sufurin jiragen saman Najeriya, Hadi Siriki ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kammala dukkanin shirye shiryen ta na gina sabon dakin saukar fasinsoji a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad dake jihar Legas.

Ministan ya bayyana ne haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki a harkokin sufurin jirage a jihar Legas.

Shashin Hausa na jaridar Leadership ta hada rahoto kamar haka;

“A cewar Karamin Ministan sufurin ma’aikatar jiragen sama Sanata Hadi Sirika, sake gina filin tashi da saukar jiragen na Murtala Muhammed ya zama wajibi, inda ya yi nuni da cewar, an gina filin jirgin na Murtala Muhammed ne yadda zai iya daukar fasinjoji guda 300,000 tun lokacin da aka gina shi.

Karamin Ministan sufurin ma’aikatar jiragen sama Sanata Hadi Sirika ya yaci gaba da cewa, amma a yanzu fasinjojin su dake yin tafiye-tagiye ta filin sun karu zuwa miliyan 8 a cikin shekaru uku da suka gabata.

Da yake yin tsokaci akan iya adadin kudin da aikin zai lashe Karamin Ministan sufurin ma’aikatar jiragen sama Sanata Hadi Sirika yace zasu kai naira biliyan 14 musamman don a yiwa filin zirgin gyaran da ya dace.

A cewar Karamin Ministan sufurin ma’aikatar jiragen sama Sanata Hadi Sirika, kafin a fara gudanar da aikin filin jirgin za’a mayar jiragen zuwa sabon gurin saukar jiragen da aka gina don su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Shi kuwa Manajin Daraktan Hukumar kula da sauka da tashin jiragen saman ta kasa FAAN shima ya sanar da cewar, za’a gusa da jiragen saman zuwa ga sabon gurinnda aka gina wanda har yanzu ake kan gufanar da sauran wasu ayyuka ake kuma sa ran kammala su kafin karshen wannan shekarar.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.