Kungiyoyin Chelsea da Arsenal zasu fafata a wasan karshen na cin kofin gajiyayyu ‘Europa League’.
Hakan na zuwa ne bayan kungiyoyin biyu suka samu nasarar a wasan gaf dana karshe wadanda suka buga yau.
Arsenal wacce ta buga wasanta a kasar Spaniya tare da kungiyar kwallon kafa ta Valencia, Arsenal ta samu nasarar jefa kwallaye 4 -2 a ragar Valencia.
Arsenal ta jefa jumillar kwallaye 7 a ragar Valencia.
Chelsea ta samu nasara ne bayan an tashi wasa 1-1 wanda ta kai ga buga bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda aka tashi CHE 4-3 FRK.
A gasar wasanni ta bana, kungiyoyin kasar Ingila sunyi fice a gasar zakarun nahiyar turai da gasar gajiyayyu ta nahiyar turan, inda kungiyar Liverpool da Totteham ne zasu barje guminsu a gasar cin kofin zakarun na nahiyar Turai.
Wasan da tin shekarar 2008, kungiyoyin kasar Ingila basu sake haduwa a wasan karshe na gasar ba.
…………………….
