(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Yan Bindiga sun sace ɗalibai mata sama da 300 a jihar Zamfara

Karatun minti 1

Rahotanni sun tabbatar da wani hari da yan bindiga su ka kai a jihar Zamfara in da suka sace dalibai mata sama da 300.

Hakan na zuwa ne kwana 8 bayan da wasu yan bindigar su ka sace dalibai a jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a safiyar Juma’a a makarantar Sakandire ta ‘yan mata da ke Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar.

Wani malamin makarantar da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da faruwa al’amarin, ya kuma ce yan bindigar sun kutsa cikin dakunan kwanan dalibai in da suka tafiya da daruruwan dalibai da yawansu ya fi 300.

Kazalika wani mazaunin garin ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewar har da ‘ya’yansa mata aka sace a makarantar.

Shi ma wani malami a makarantar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Jaridar Daily Nigerian cewar a kalla dalibai 500 aka sace.

Malamin ya ce a ranar Alhamis da daddare, kimanin dalibai 600 ne a cikin makarantar, in da ya ce da safiya bayan kiran rijista, dalibai 100 kadai a ka iya samu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog