Jami’an DSS sun ‘kama’ Salihu Tanko Yakasai bayan kalaman sukar Buhari

Karatun minti 1
Salihu Tanko Yakasai

Rahotanni daga wasu majiyoyi sun tabbatar da batan Salihu Tanko Yakasai, daya daga cikin mashawartan gwamnan Kano, Dr Abdullahi Ganduje.

Salihu ya yi tsokacin ne bayan labaran sace ‘yan mata sama 300 a makarantar Sakandire da ke jihar Zamfara.

An zargi jami’an hukumar DSS da kama Salihu a daren jiya Juma’a.

DABO FM ta tattara cewar, Salihu Yakasai ya yi kakkausan suka ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Ya ce gwamnatocin APC na kowane mataki sun gaza samar da babban muhimman abu da aka zabe su domin su samar.

Wannan ne karo na biyu da Salihun ya yi irin wannan kalami, a karon farko da ya fura irin zancen, gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shi daga mukaminsa.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog