(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Abubuwan fashewa sun fashe a Igabin jihar Kaduna, sun jikkata yara 7

Karatun minti 1

Wasu abubuwan fashe da ba a san ko mene ne ba sun tashi a unguwar Mangwaro ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewar fashewar abubuwan ya yi sanadiyyar jikkata wasu yara guda bakwai a unguwar da ke ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Sameul Aruwan ne ya sanar da afkuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar da yammacin Talata.

Ya ce jami’an tsaro sun ce fashewar abin ya ritsa da yaran ne bayan da suka ɗauki abin fashewar suka yi ta wasa da shi ba tare da sun san ko mene ne ba.

Ya ce a yanayin hakan ne yaran suka tafi da shi kusa da gidajensu har tsautsayi ya ja abin ya fashe ya illata su.

“Yara 7 yanzu haka suna karɓar kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika.

Kwamishinan ya ce gwamnan jihar, Mallam Nasiru El Rufai, ya umarci jami’an tsaro da su tsananta bincike a kan lamari, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su zama masu lura da abubuwan da ke zagaye da su.

Gwamnatin ta kuma fitar da wasu lambobi da ta ce mutane za su kira a duk lokacin da suka ga abin da ba su yadda da shi ba.

Lambobin su ne 09034000060 da 08170189999.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog